1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An samu musayar ra'ayi a kasar Afghanistan

Zulaiha Abubakar
August 26, 2018

Shugaban kasar Afghanistan Ashraf Ghani ya ki amincewa da takardun ajiye aiki da wasu manyan jami'an tsaron kasar suka mika masa.

https://p.dw.com/p/33mVN
Afghanistan, Präsident, Ashraf Ghani in Kabul
Hoto: Reuters/M.Ismail

Tun fari mai bai wa shugaban kasar shawara a fannin tsaro ne ya fara shelar ajiye aiki, kafin daga bisani ministocin tsaro da na cikin gida da kuma kwamandan da ke jagorancin duk fannonin tsaron kasar su mika wa ofishin shugaban kasar takardun barin aiki ba tare da sun bayyana hujjojin su ba, da yake mayar da martani kakakin fadar mulkin kasar Haroon Chakansuri ya bayyana cewar Shugaba Ashraf Ghani ya yi watsi da wannan bukata tare da ba su umarnin komawa bakin aiki .

Wannan danbarwa ta kunno kai ne tsakanin shugaban kasar da jami'an tsaro lokacin da hankula suka fara kwantawa a kasar, bayan wani jerin kwanaki uku da 'yan ta'adda suka yi a wasu biranen kasar suna daukar hotuna da jami'an tsaro cikin raha.