Jami′an tsaro sun kama mutane 900 a Senegal | Labarai | DW | 25.01.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jami'an tsaro sun kama mutane 900 a Senegal

Hukumar 'yan sandan Senegal ta sanar a wannan Litinin din cewa, ta kama mutane a kalla 900 a wani bincike da ta aiwatar a tsarinta na yaki da ta'addanci a kasar.

Wannan bincike dai ya gudana ne a karshen makon da ya gabata sakamakon yawaitar hare-hare da ake samu a yankin Yammacin Afirka inda a ranar 20 ga watan nuwamba wasu 'yan ta'adda suka kai hari a wani babban Hotel na birnin Bamako, sannan a ranar 15 ga wannan wata na Janairu a wani babban Hotel na birnin Ouagadougou abun da ya kai hukumomin na Senegal ga daukan wannan mataki na riga kafi.

A ranar 21 ga wannan watan ne dai ministan cikin gidan kasar ta Senagal ya sanar a gaban 'yan majalisun dokokin kasar cewa ya baiwa jami'an tsaron kasar izinin aiwatar da wannan bincike.