1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hukumar kare bil'Adama ta ce 'yan doka na kashe jama'a

Abdoulaye Mamane Amadou
April 16, 2020

Hukumar kare hakin bil'Adama ta Najeriya ta ce jami'an tsaron kasar sun halaka mutane 18 a yunkurinsu na bin matakan da hukumomin kasar suka dauka na takaita zirga-zirga.

https://p.dw.com/p/3b06m
Nigeria Polizei
Hoto: Getty Images/AFP/P. Utomi Ekpei

A cikin wani rahoton da ta wallafa a yammacin jiya, hukumar kare hakin bil'Adama ta Najeriya ta ce mutane akalla mutun 105 ne jami'an tsaron Najeriya suka ci wa zarafi haka ba tare da shari'a ba a yayin da wasu 18 suka mutu a yunkurinsu na tabbatar da doka da oda ga matakin takaita zirga-zirga da hukumomin Najeriya suka kakaba.