1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kasar Amirka na zargin Cuba akan jami'anta na Diplomasiyya

Zulaiha Abubakar
June 28, 2018

Rahotanni daga hukumar tsaron kasar Amirka sun bayyana samun jami'in diplomasiyyar kasar da kamuwa da bakuwar cuta a kasar Cuba kamar yadda hukumar lafiyar Amirka ta sanar yau Alhamis.

https://p.dw.com/p/30VBF
Kuba Eröffnung der US Botschaft in Havanna
Hoto: Reuters/A. Meneghini

Ta kuma kara da cewar wannan ne karo na biyu da bincike ya tabbatar da jami'an Ddplomasiyyar Amirka da ke aiki a kasar ta Cuba wadanda ke zaune a wata unguwa da akayi tanadi don su sun kamu da wannan cuta, tun bayan billar irin ta da aka taba samu a shekara ta 2017,lamarin ya kawo adadin  Amirkawan da suka kamu da cutar zuwa 26. Likitocin Amirka sun bayyana nau'in cutar da cewar ya hada da juyewar tunani,da take kare kanta gwamnatin kasar Cuba ta ce ba ta da masaniya a kan wannan batu amma za ta gudanar da bincike.