1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An tsaurara binciken tsaro a Sri Lanka

Zulaiha Abubakar
April 28, 2019

Binciken jami'an tsaro ya tabbatar da yadda Zahran Hashim yayi amfani da hanyar koyar da 'ya'yan masu hannu da shuni karatun addini wajen cusa musu akidar kai harin da yayi sanadiyyar rasa rayuka a kasar.

https://p.dw.com/p/3HamH
Sri Lanka Terrorismus l nach den Anschlägen
Hoto: picture-alliance/dpa/M. Swarup

Da safiyar wannan Lahadin mahukuntan kasar Sri Lanka karkashin jagorancin shugaban kasa da Firaiminista suka jagoranci tawagar wasu jama'a don gudanar da addu'a ta musamman ga wadanda harin ya rutsa da su, yayin addu'oin babban jagoran darikar Katolika na kasar Cardinal Malcolm Ranjith ya bayyana harin a matsayin wulakanta 'dan Adam daga nan sai yayi addu'ar dorewar zaman lafiya da fahimtar juna tsakanin mabiya addinai a fadin kasar. Da yake bada hakuri ga jama'a firaministan kasar Ranil Wickremesinghe ya bayyana yadda jami'an tsaro suka yi nasarar kashe mafiya yawan wadanda ke da hannu a mumman harin tare da tsare da dama daga cikinsu don fadada bincike. Wuraren ibadar mabiya addinin Kirista a kasar sun kasance a rufe saboda fargaba.