Jamhuriyar Benin ta tuno zamanin bayi
Babu shakka tarihin Jamhuriyar Benin ba zai cika ba, ba tare da ambaton cinikin bayi ba, lokacin da shugabanni suka sayar da fursunonin siyasa ga Turawa. Yanzu kasar na kokarin sanyaya wahalar da aka sha a baya.
Birnin Ouidah mai dumbin tarihi
Hatta mashigar wannan birnin na dauke da sako mai karfi. Yayin da wasu biranen ke boye labarai masu tayar da hankali da suka shude, wannan birni na Ouidah, ya fitar da nashi ne karara. Harkokin cinikin bayi zuwa kasashen yamma sun yi matukar tasiri a wannan waje daga karni na 16 zuwa karni na 19.
Gani na karshe
Bishiyoyin kwakwa da ke gabar ruwan Ouidah, su ne abubuwan da ke zama na karshe da bayi da aka kwashe daga Afirka zuwa kasashen Turai suka a nahiyarsu ta gado. Nan ne inda masu cinikin bayi daga kasashen Portugal da Faransa da ma Birtaniya suka kwashi miliyoyin Afirkawa zuwa yankunan Amirka. Shugabannin gargajiya ne suka sayar da mutanensu ga turawan.
Karfafa al'adar tuna baya
Shekarun 1990 sun sauya yadda ake tunawa da wannan tarihi mara dadi a Benin. An mika wa hukumar UNESCO ''Porte du Non-Retour'' Kofar kare kukanka, don zama wajen tunawa da cinikin na bayi. An kuma gudanar da taron duniya kan lamarin a 1999, wanda ya sanya shugaban kasa na wancan lokaci Mathieu Kerekou zuwa yankin Baltimore na Amirka, inda ya nemi gafara daga wasu daga cikin tsatson bayin na da.
Daga matsayin fadar mulki zuwa gidan tarihi
Sabon gidan adanan tarihi na birnin Ouidah waje da aka gina a tsohon mazaunin masu 'yan Portugal da suka yi mulki. Yana daga cikin ayyukan da Shugaba Patrice Talon ya jagoranta don nazarin tarihin Jamhuriyar Benin. Galibin 'yan kasar na da alaka da iyalan da cinikin bayi ya shafa ko wadanda suka azaftar da su. Shi ma Shugaba Talon an yi zargin alakarsa da daya daga ciki bangarorin biyu.
Tarihin wadanda suka aikata zaluncin
Da dama sun yi amannar cewa dole ne a rika bayyana wannan tarihin mai ban takaici muddin dai ana son samun sasanci a wannan kasa. Amma hakan zai wani amfani ne? Tun cikin watan Agusta, masu ziyara suka yi ta ganin kayayyaki na wadannan tsoffin masarautu na Ouidah da kuma Dohamey, wadanda duk ke da alaka da cinikin bayin.
Hanyar da ake bi da bayi daga birnin Ouidah
Ministan al'adun Jamhuriyar Benin, Jean-Michel Abimbola, ya ce kasar ta ware dala bilyan 1.8 domin wasu ayyuka kamar gina wuraren adana tarihi da za su taimaka wa kasar ta farfado da wahalhalun baya. Ana maraba da baki daga ketare ciki har da makwabciya Najeriya. Sai dai yanzu lokacin corona, yawanci masu zuwa na cikin gida ne da ke da sha'awar su fahimci kasarsu da kyau.