SiyasaAfirka
Dakarun gwamnati sun samu nasara Afirka ta Tsakiya
February 12, 2021Talla
A cikin sanarwar da firaministan kasar ya fitar ya ce nasarar ceto garin mai suna Beloko daga hannun kawancen 'yan tawayen kasar a yanzu ta ba su damar bude babbar hanyar da ta hada kasar ta Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da kasar Kamaru, yana mai cewa za su tabbatar jama'a na zirga-zirga cikin kwanciyar hankali.
Kungiyoyi masu rike da makamai akalla guda shida ne dai a kasar suka hada karfi suke yakar gwamnatin kasar tun a watan Disambar da ya gabata, kuma duk da cewa dakarun gwamnati sun samu nasarori, har kawo yanzu rahotanni na cewa 'yan tawayen sune ke da iko da kaso biyu cikin uku na kasar ta Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya.