1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamhuriyar Afirka ta Tsakiya

Shirin Zabe a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya

Mimi Mefo ARH/LMJ
December 26, 2025

A ranar Lahadi 28 ga watan Dismabar 2025, za a gudanar da zabe a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiyya ciki har da na shugaban kasar da Shugaba Faustin-Archange Touadera ke neman yin tazarce a wa'adi na uku.

https://p.dw.com/p/5606e
Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya | Zabe | Shugaba Faustin-Archange Touadera | Tazarce
Shugaba Faustin-Archange Touadera na Jamhuriyar Afirka ta TsakiyaHoto: Olga Maltseva/AFP

Za a gudanar da zaben ne a karkashin kulawar Rundunar Wanzar da Zaman Lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya MINUSCA, wadda ta ce za ta samar da tallafin kayan aiki da tsaro, a lokacin zaben da ake ganin zai gudana a bana. Zaben da ke zuwa, bayan yin kwaskwarima a kundin tsarin mulki duk da korafin 'yan adawa.

Ana dai hasashen cewa, Shugaba Faustin-Archange Touadera da ke neman tazarce a karo na uku ne zai samu nasara a zaben shugaban kasa, kasar da ke yanki tsakiyar Afirka da ba ta da iyaka da teku kana daya daga cikin kasahe mafi talauci a duniya da yanayin tsaro ya lafa bayan yakin basasar da aka yi a shekara ta  2010.

Murkushe masu rike da makamai

A cewar masu lura da al'amura da dama, sojoji tare da goyon bayan sojojin haya daga kungiyar Wagner ta Rasha, sun tilasta wa kungiyoyin 'yan tawaye masu dauke da makamai wadanda suka kawo cikas ga zaben da aka yi a karshen shekara ta 2020 ja da baya. Mai shekaru 68 a duniya, Shugaba Touadera da aka  zaba a farkon shekara ta 2016 kuma aka sake zabarsa a zagaye na farko na zabe a shekara ta 2020 da a ciki 'yan adawa suka yi zargin magudi, ana ganin har yanzu shi ne zai samu nasara.

Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya | Zabe | Jagoran Adawa | Anicet-Georges Dologuélé
Jagoran adawar Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya Anicet-Georges DologuéléHoto: Getty Images/AFP/I. Sanogo

'Yan takarar shugaban kasa bakwai ne za su fafata, wadanda daga cikinsu ake ganin biyu ne abokanan hamayyar Touadera wato: Anicet-Georges Dologuélé jagoran ‘yan adawa da ya zo na biyu a wancan zaben da Henri-Marie Dondra, 'yar takarar jamiyyar UNIR kana tsohuwar firaminista. Yanzu haka dai, 'yan adawar suna nuna damuwa a kan zaben, inda suke zargin  za a tabka magudi. Gamayyar jam'iyyun adawa ta ma sanar da kauracewa zaben, saboda abin da ta kira rashin gaskiya kamar yadda Anicet Georges Dologuélé jagoran 'yan adawar ya nunar.

Cimma nasarori da samar da ci-gaba?

Shugaba Touadera dai ya kafe ga irin aikin da yayi na samun nasara, wanda a cikin hirarsa da DW shugaban ya ce: "Zuwansa kan karagar mulki an samu ci-gaba a Jamhriyar Afirka ta Tsakiya." A karshen watan Nuwamba, mataimakin sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya kan ayyukan zaman lafiya Jean-Pierre Lacroix da ya kai ziyara a birnin Bangui ya yi furcin cewa: "Yanayin tsaro ya inganta, kana an sami ci-gaba mai mahimmanci a Jamhuriyar ta Afrika ta Tsakiya."


 

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani