Jama′a na cikin zaman fargaba a Abuja | Labarai | DW | 26.06.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jama'a na cikin zaman fargaba a Abuja

Mutane a ƙalla 21 suka mutu yayin da wasu da dama suka jikata a hare-haren bama-bamai da aka kai a yammancin jiya a Abuja babban birnin Najeriya.

Wasu da suka shaida lamarin sun ce bam ɗin ya fasa tagogin shagunan da ke kusa sannan ya ta da wani baƙin hayaƙi. Bam ɗin ya tashi ne a wani wuri da ke kusa da cibiyar hada-hadar ciniki ta Banex Plaza da ke unguwar Wuse 2.

Har yazuwa yanzu 'yan sanda ba su haƙiƙance ba addadin mutanen da lamarin ya rutsa da su, sannan kuma babu wata ƙungiya da ta ɗauki alhakin kai harin. Hukumar leken asiri ta Najeriya ta ce an kama ɗaya daga cikin waɗanda suka ɗana bam ɗin. Yayin da ɗaya,sojoji suka harbe shi har lahira a lokacin da yake ƙoƙarin tserewa.

Mawallafi: Abdourahamane Hassane
Edita : Usman Shehu Usman