1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jakadar Amirka a Majalisar Dinkin Duniya ta aje aiki

Yusuf Bala Nayaya
October 9, 2018

Jakadar Amirka a Majalisar Dinkin Duniya Nikki Haley za ta bar kujerar da take kai nan da karshen wannan shekara. Ita tare da Shugaba Donald Trump suka bayyana haka a wannan Talata.

https://p.dw.com/p/36FQ1
US-Botschafterin der Vereinten Nationen Nikki Haley
Hoto: picture-alliance/dpa/S.Wenig

Nikki Haley ba ta dai yi karin haske ba kan dalilanta na sauka daga mukamin, ko da yake akwai rade-radin cewa za ta dawo kan harkokin na gwamnati ko siyasa nan gaba.

Sai dai cikin raha ta katse hanzari na 'yan jarida inda ta ce ba ta da buri na takarar shugaban kasa: "A 'a ba ni da buri na takarar shugabar kasa a 2020 sai dai zan mara baya ga Trump."

Shi kuwa Shugaban na Amirka Trump ya bayyanata a matsayin jajirtacciyar abokiyar aiki wacce Amirka ba za ta manta da ita ba saboda irin gudunmawar da ta bayar wajen ci gaban kasa musamman a lokacin da ta yi gwamna da ma wakilcin na Amirka tsakanin kasa da kasa. Trump ya ce dama watanni shida da suka gabata ta fada masa tana son ta ajiye mukamin ta dan huta.

.