Ku biyo mu domin jin yadda wata matashiya ta yi gwagwarmayar kammala karatunta, a al'ummar da har yanzu ake ci gaba da fifita maza. Ilimi dai shi ne ginshiƙin ci gaban kowace al'umma, kuma yana da muhimmanci a ba wa yara mata damar samun ilimin zamani.