Jagoran adawan Kongo zai tsaya takaran shugaban kasa | Labarai | DW | 13.03.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jagoran adawan Kongo zai tsaya takaran shugaban kasa

Jagoran adawa na Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kongo, Moise Katumbi ya ce zai koma kasar don tsayawa takarar kujerar shugabancin kasar a babban zaben da aka shirya yi a watan Disamba.

Katumbi da ake zargi da laifin cin amanar kasa, ya sanar cewa a watan Yuni zai koma kasar daga Afrika ta Kudu inda ya ke samun mafaka bayan rigingimun da suka biyo bayan zargin da ake ma sa a wancan lokacin. Katumbi wanda shi ne ya kasance babban dan takara kujerar shugaban kasar daga bangaren adawa, ya sha fuskantar shari'a bisa zarginsa da gwamnati ta yi na dauko sojojin haya daga ketare domin fada a kasar.

An sha jinkirta zaben kasar amman yanzu an tsara gudanar da zaben a watan Disamba wannan shekarar da muke ciki. Gwamnati  ta ce ta jinkirta zaben sau da dama bisa karancin kudi da kasar ke fuskanta. Kongo dai ta sha fama da ringinmu da suka yi sanadiyar salwantar rayuka tun bayan da shugaba Joseph Kabila ya ki amincewa da ya sauka daga mulki bayan cikar wa'adinsa.