1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jagoran adawa ya lashe zaben Maldibas

Yusuf Bala Nayaya
September 24, 2018

Ba zato ba tsammani dai shugaban ya sha kaye, lamarin da ya haifar da shiga yanayi na tsallen murna da shewa a tsakanin al'ummar wannan kasa da ke zama tsibiri na masu zuwa shakatawa a Tekun Indiya.

https://p.dw.com/p/35Nlw
Malediven Ibrahim Mohamed Solih
Ibrahim Mohamed Solih ya lashe zaben shugaban kasa a MaldibasHoto: Reuters/A. Faheem

Shugaban kasar Maldibas Abdulla Yameen ya amince da shan kaye a zaben shugaban kasar da aka gudanar.

A jawabin da ya yi wa al'ummar kasar ta akwatunan talabijin Yameen yace zai shirya mika mulki cikin ruwan sanyi ga sabon zababben shugaban kasar Ibrahim Mohammed Solih.

An dai ta nuna fargaba ko shugaban kasar ba zai amince da shan kaye ba.

Sakamakon hukumar zabe dai ya nunar da cewa Ibrahim Mohamed Solih jagora na adawa ya samun kashi 58.3 cikin dari na kuri'un da aka kada inda ya bai wa abokin hamaiyarsa tazara mafi girma da aka gani a zabe tun bayan komawar kasar kan tafarkin dimukuradiya a 2008.

Kusan kashi 90 cikin dari na masu zabe 262,000 ne dai a Maldibas suka kada kuri'unsu inda wasu suka share sama da sa'oi biyar suna jira a kan layi.