1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jagoran adawar Kwango ya koma gida

Yusuf Bala Nayaya
August 1, 2018

Jagoran adawa a Kwango Jean-Pierre Bemba ya koma kasarsa a wannan rana ta Laraba bayan shekaru goma tsare a gidan kaso a birnin The Hague.

https://p.dw.com/p/32S0C
Kongo Ankunft Oppositionsführer Jean-Pierre Bemba
Hoto: Reuters/J. R. N'Kengo

Jean-Pierre Bemba ya koma gidan ne inda kuma zai tsaya takara don kalubalantar Shugaba Joseph Kabila a zaben watan Disamba.

Bemba da kotun daukaka kara ta yi fatali da hukuncin da kotun ICC ta yi masa, ya sauka a filin jiragen sama na N'Djili na birnin Kinsasha inda ya samu tarba ta dubban magoya bayansa sanye da riguna da huluna dauke da hotonsa.

Ya dai sauka a filin jiragen saman ne sanye da kwat da jan lakatayen, ya gaisa da iyalai da mambobi na jam'iyyar MLC kafin ya kama hanyar zuwa cikin birnin na Kinsasha inda dubban magoya baya suka tarbe shi duk da cewa sun gamu da fushin 'yan sanda wadanda suka harba masu hayaki me sa hawaye.