1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Salon rayuwaAfirka

Jadawalin zaben Afirka ta kudu ya ja hankalin jaridun Jamus

Mouhamadou Awal Balarabe
February 23, 2024

Sabanin shekarun baya, da kamar wuya jam'iyyar ANC mai mulki a Afirka ta Kudu ta samu rinjaye a zaben gama gari sakamakon kura-kurai da ta tafka da kuma karuwar rashin aiki yi, a cewar daya daga cikin jaridun Jamus.

https://p.dw.com/p/4ckoH
A Mayun 2009 ne aka gudanar da zaben karshe a Afirka ta Kudu
A Mayun 2009 ne aka gudanar da zaben karshe a Afirka ta KuduHoto: Reuters/M. Hutchings

die tageszeitung ta mayar da hankali kan jadawalin zaben Afirka ta Kudu, inda ta ce Shugaba Cyril Ramaphosa ya tsayar da 29 ga watan Mayun 2024 a matsayin ranar da za a gudanar da zaben gama da gari a kasar. Mai yiyuwa ne a kawo karshen gwamnatin ANC wacce ta shafe shekaru 30 tana mulki, amma babu wani tabbas game da wanda zai yi nasara a zaben ‘yan majalisar dokokin 400 da gwamnatocin larduna tara na Afirka ta Kudu.

Nelson Mandela ya taimaka wa ANC lashe zaben Afirka ta Kudu a1994
Nelson Mandela ya taimaka wa ANC lashe zaben Afirka ta Kudu a1994Hoto: picture alliance/AP Photo/j. Parkin

Jaridar ta ce a ranar 27 ga Afrilun 1994, ANC  karkashin Nelson Mandela ta samu kashi 62% na kuri'un da aka kada. Amma kuri'ar jin ra'ayin jama'a na baya-bayan nan ta nuna cewa babu hadin kai da sulhu tsakanin al'umma, sannan talauci ya shafi sama da kashi 55% na al'ummar Afirka ta Kudu da kashi 33%i na rashin aikin yi a tsakanin matasa.

Karin bayani:Shugaba Ramaphosa na shirin yin tazarce 

Masu jefa kuri'a a runfuna 9,000 na birane da karkara na Afirka ta Kudu sun kara nesanta kansu ga jam'iyyun siyasa saboda rashin cika alkawura. A karon farko ANC za ta iya samun kashi 40%, yayin da jam'iyyr adawa mafi karfi DA za ta iya tashi da 19% , ita kuwa EFF za ta iya samun 16% na kuri'un da za a kada.

Sojojin Guinea na karyawa inda ba gaba

Kanar Mamady Doumbouya da wasu sojoji da ke da karfin fada a ji a Guinea
Kanar Mamady Doumbouya da wasu sojoji da ke da karfin fada a ji a GuineaHoto: Kommunikationsdienst der Präsidentschaft von Guinea

Frankfurter Allgemeine Zeitung ta tsara sharhi mai taken " Sojojin Guinea sun yi hawan kawara" inda ta ce gwamnatin mulkin soji ta kori daukacin ministocin tare da kwace fasfonsu da asusunsu na bankuna, lamarin da ya kara dagula yanayin siyasar kasar. fadar mulki ta Conakry ta bukaci ministocin da aka sauke da su mika motocinsu na aiki ga fadar shugaban kasa.

Karin bayani: Guinea Conakry: Shakku kan alkawarin zabe

Jaridar da ke da mazauni a birnin Frankfurt ta ce rushe gwamnatin ta farar hula ya sa an tsananta matakan tsaro, musamman a babban birnin kasar Conakry. Sojoji sun kafa shingayen bincike tare da yin sintiri a kan tituna. Sannan zanga-zangar nuna adawa da rusa gwamnati ta haifar da tashin hankali a wata gundumar babban birnin Guinea, inda jandarmomi suka harbe wasu daliban makarantar sakandare biyu har lahira.

An samu mace-mace a Conakry a tashin hankalin da ya biyo bayan rusa gwamnati
An samu mace-mace a Conakry a tashin hankalin da ya biyo bayan rusa gwamnatiHoto: Abdoulaye Sadio Diallo/DW

Babban abin mamakin ma a cewar jaridar, shi ne rufe iyakokin Guinea da gwamnatin mulkin soji ta yi don abin da ta kira guje wa katsalandan na kasashen waje musamman tsuhuwar uwar gijiyarta Faransa. Tun bayan juyin mulkin watan Satumba 2021 ne, sojoji karkashin jagorancin Kanar Mamady Doumouya ke mulki a Guinea, bayan hambarar da Alpha Condé da ya kwaskware kundin tsarin mulkin kasar don samun damar yin tazarce.

Afirka na fama da zagon kasa daga Daular Larabawa

Neue Zürcher Zeitung  ta yi sharhinta ne mai taken "Hadaddiyar Daular Larabawa na tada zaune tsaye a Afirka", inda ta ce rawar da kasashen da ke da matsakaicin karfin tattalin arziki ke takawa a Afirka na nuna yadda tsarin dangantaka tsakanin kasa da kasa ya canza. Kuma wannan na haifar wa kasashen yammacin duniya kalubale.

Karin bayani: Juyin mulki a Afrika gazawar dimukuradiyya

Tashar jirgin ruwan Jibouti ta samu tallafin Hadaddiyar Daular Larabawa
Tashar jirgin ruwan Jibouti ta samu tallafin Hadaddiyar Daular LarabawaHoto: YASUYOSHI CHIBA/AFP

Jaridar ta ce Hadaddiyar Daular Larabawa ta samu karfin fada a ji a cikin shekaru goma da suka gabata a kasashen Larabawa na Afirka. Ko da bayan da guguwar neman sauyi ta kada a 2011, Hadaddiyar Daular Larabawa ta taimaka wajen kitsa juyin mulkin da ya hambarar da mulkin Mursi tare da maye gurbinsa da na ministan tsaro na lokacin Abdelfatah al-Sisi. Yankin kudu da hamadar Sahara ma ya kasance a komar wannan kasa saboda dama kogi ne ya raba su.

 Sai dai a daya hannun, Neue Zürcher Zeitung ta ce Hadaddiyar Daular Larabawa ta zuba biliyoyin daloli don yi wa tashoshin jiragen ruwa na wasu kasashen Afirka kwaskwarima. Amma tana dagula zaman lafiya a wasu kasashen Afirka don cimma muradinta na diflomasiyya. Hasali ma, tana da hannu a wasu rikice-rikice inda a wasu lokuta take amfani da hanyoyi masu kama da na Rasha. Mafi kyawun misali shi ne hannun da take da shi a rikicin kasar Sudan.