Jadawalin zabe a Masar | Labarai | DW | 09.07.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jadawalin zabe a Masar

Shugaban Masar mai rikon kwarya Adli Mansour ya yi alkawarin shirya zabe kan nan da watan Janairu mai zuwa, bayan an kwaskware kundin tsarin mulki.

Shugaban Masar mai rikon karya Adli Mansour ya dibar wa kansa wa'adin watannin shida domin gudanar da sabbin zabukan da za su mayar da kasar kan turbar demokaradiya. Cikin wata sanarwa da ya fitar shugaban ya ce ya rigaya ya nemi kwararru a fannin shari'a su zauna kan nan da kwanaki 15 masu zuwa domin kwaskware kundin tsarin mulkin kasar ta Masar.

Adli Mansour ya dauki wannan matakin ne sa'o'i kalilan bayan da mutane 51 da ke goyon bayan hambararren shugaba kasa suka rasa rayukansu, a kusa da barikin sojoji da ake kyautata zato ya na tsare. Magoya bayan Mohamed Mursi sun yi ikirarin cewa an afka musu ne da fada a daidai lokacin da suke tsaka da sallah. Sai dai kuma sojoji sun karyata wannan zargi, inda suka ce bangaren 'yan uwa musulmi ne suka fara bude musu wuta. . Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon ya yi kira da a kafa kwamitin bincike mai zaman kansa domin tantance zahirin abin da ya faru.

Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Umaru Aliyu