1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afirka ta Kudu: Jacob Zuma ya kaurace wa shari'a

Abdourahamane Hassane
July 19, 2019

Tsohon shugaban Afirka ta Kudu Jacob Zuma ya daina ba da hadin kai ga hukumar da ke gudanar da bincike a game da zargin da ake yi masa na cin hanci.

https://p.dw.com/p/3MKeK
Nigeria Nationalversammlung Abuja
Hoto: AFP/Getty Images/P. Ojisua

Wani lauyan da ke kare tsohon shugaban ya bayyana wa hukumar a birnin Johannesburg cewar ba za su ci gaba da ba da hadin kai ba saboda nuna fifiko da hukumar ke yi,da kuma yada ya ce shaidu a gaban hukumar ke tozarta tsohon shugban. Ana dai zargin tsohon shugaban da laifin cin hanci da wani kamfanin na 'yan Indiya na Gupta a zamanin mulkinsa daga shekara ta 2009 zuwa 2018.