1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zuma ya musanta aikata ba dai-dai ba da iyalan Gupta

Binta Aliyu Zurmi MNA
July 15, 2019

A lokacin da ya gurfana gaba shari'a wannan Litinin tsohon shugaban Afirka ta Kudu Jacob Zuma ya musanta duk wasu zarge-zargen cin hanci da almundahana da dukiyar kasa da ake masa.

https://p.dw.com/p/3M6mZ
Südafrika Prozess gegen Jacob Zuma in Durban
Hoto: Reuters/N. Bothma

Tsohon shugaban kasar Afirka ta Kudu Jacob Zuma ya nisanta kansa daga duk wasu zarge-zargen cin hanci da almundahana da dukiyar kasa da ake masa.  Ana dai zargin Zuma da yin sama da fadi da kudin kasar a yayin da yake kan karagar mulki.
 
Da yake ba da na sa ba'asin a gaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kasar da aka gurfanar da shi a wannan Litinin, Jacob Zuma ya ce kazafi kawai ake masa, inda ya ce ba shi da wata alaka da ta saba doka da iyalan Gupta kuma an yi hakan ne kawai domin a bata masa suna.

Mai shekaru 77 a duniya Zuma na fuskantar tuhumar aikata cin hanci ne, zargin da ya haifar da cece-ku-ce a matakin kolin jam’iyyarsa ta ANC mai mulkin kasar, wanda daga bisani mambobinta suka tilasta masa yin marabus.