Ja in ja kan maye gurben Merkel | Labarai | DW | 11.04.2021
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ja in ja kan maye gurben Merkel

Bangarorin da ke takaddama kan maye gurbin shugabar gwamnatin Jamus na ci gaba da jayayya kan tantance wanda zai tsaya takara da sunan kawancen masu mulki.

Mutanen nan biyu da ake hasashen daya zai maye gurbin shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel wato Armin Lasche na jam'iyyar CDU da Markus Söder na CSU za su yi wata ganawar sirri a yau Lahadi, da kusoshin kawancen jam'iyyun na CDU da CSU masu mulkin Jamus a birnin Berlin.

Ana dai fama da tababa kan wanda zai maye gurbin shugbar gwamnati da ke shirin bankwana da mulki a wannan shekara, tsakanin Armin Laschet da yanzu hakan ke jagorancin jamiyyar CDU ta Misis Merkel da abokin hamayyarsa Markus Söder na jam'iyyar CSU mai kawance da ita.

Bangarorin biyu dai za su tattauna ne kan batun sabonta tarayyar Jamus nan da gaba, to amma sai da dama na ganin da akwai rarrabuwar kawuna kan tantance mutanen biyu, duk da yake Markus Söder na kara samun kwarjini da goyon bayan 'yan majalisar dokoki daga kawancen masu mulkin.