Izra′ila ta kashe Palesdinawa 64 a Gaza | Labarai | DW | 10.07.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Izra'ila ta kashe Palesdinawa 64 a Gaza

Rikici tsakanin Izra'ila da Hamas na ci gaba da ruruwa inda aka shiga kwana ta uku ta luguden wuta a Zirin Gaza. Lamarin da ke lamshe rayuka tare da lalata kadarori.

Dakarun Izra'ila sun shafe dare suna barin wuta ta sama a zirin Gaza inda a cikin kwanaki uku suka hallaka Palesdinawa kimanin 64. Rahotannin da ke zuwa mana daga yankin Gabas ta Tsakiya sun nunar da cewa a daren Laraba zuwa Alhamis, Palesdinawa 14 suka rasa rayukansu a hare-haren da dakarun Izra'ila ke kai musu.

Ita dai gwamnatin Izra'ila ta ce ta dauki wannan matakin ne domin ladabtar da 'yan Kungiyar Hamas da ke kai mata da hare-hare da rokoki. Manzon Palesdinu a Majalisar Dinkin Duniya Riyad Mansoor ya yi kira ga kwamitin sulhu da ya yi zaman gaggawa domin yin nazarin halin da ake ci tsakanin Izra'ila da kuma yankinsu.

Shi ma sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-Moon ya nuna fargaba dangane da salon da rikici tsakanin Izra'ila da Palesdinawa ke dauka.

"Ina cikin damuwa dangane da tanshin hankali da ake fama da shi a zirin Gaza da Kudancin Izra'ila da kuma a yamma da Kugin Jordan ciki har da gabashin birnin Kudus. Wannan shi ne rikici mafi muni da ake fuskanta a shekarun baya-bayannan a wannan yanki, lamarin da na yi Allah wadai da shi. An harba rokoki da dama daga zirin Gaza zuwa Izra'ila. Dole a kawo karshen wadannan hare-hare. Sannan kuma ina kira ga firaministan Izra'ila Benjamin Netanyahu da ya kai hankali nesa, tare mutunta dokokin kasa da kasa da suka tanadi kare fararen hula."

Mawallafi: Mouhamadou Awal Balarabe
Edita: Umaru Aliyu