1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Samamen Izra'ila a cibiyar atsayen sojojin Hamas

February 13, 2023

Jami'an tsaron kasar Izra'ila sun kai samamen ramuwar gayya a cibiyar horar da sojojin Hamas da ke Zirin Gaza.

https://p.dw.com/p/4NOjz
Luftangriff auf den Gaza Streifen
Hoto: Majdi Fathi/ZUMAPRESS.com/picture alliance

A cikin wani sakon Twitter da jami'an tsaron Izra'ilar suka wallafa a wannan Litinin sun bayyana cewa sun kai wannan samame ne a daren Lahadi wayewar Litinin a matsayin martani bayan harba wa kasar roka daga yankin Palestinu.

A yayin samamen dai jiragen yaki sanfarin Tsahal mallakar Izra'ila sun yi kaca-kaca da cibiyar horo da kuma kera rokoki da ke karkashin kasa mallakar kungiyar 'yan ta'addata ta Hamas a fardarsu sai dai ba tare da sun yi wani karin bayani ba kan irin barnar da suka yi.

A 'yan kwanakin nan dai rikici tsakanin Izra'ila da Falasdinu na dada yin kamari, lamarin da ya sa kasashen duniya da dama yin kiraye-kiraye da su kwantar da hankulansu duba da karuwar tashe-tashen hankulan na haifar da mace-macen mutane a bangorin biyu.