Nijar da Italiya sun karfafa huldar diflomasiyya
January 4, 2018Kasar Italiya zata taimaka wa kasar Nijar a fannin tsaro da kwararar bakin haure domin tallafawa kokarin gwamnatin na shawo kian kalubalen da ta ke fuskanta a wadannan fannoni.
Ministan harkokin wajen kasar Italiya, Angelino Alfano ya sanar da hakan yayin kammala ziyarar da ya kai Nijar bayan ganawar da shugabanni da hukumomin kasar.
Ya ce tun a shekarar da ta gabata gwamnatocin kasashen biyu suka kulla yarjeniyoyi wadanda ake fatan zartar da su nan bada jimawa.
Abinda ya shafi tsaro a cewar ministan kula da tsaron Nijar Kalla Moutari, babban al‘amari ne.
Yace kasar Italiya z ata taimaka ta fannin tsaro da kayan aiki da suka hada da makamai da kuma horar da dakarun Nijar dabarun yaki da 'yan ta'adda. Ya kiyasata kudin kayayyakin da cewa sun kai CFA miliyan dubu 35
Minsta Kalla ya kuma karyata zargin cewa kasar Italia za ta kawo sojojinta cikin Nijar.
A nata bangaren jakadiyar Nijar a Kasar Italiya Madam Ingade Nana Hadiza Noma kaka, ta ce karfafa hulda tsakanin kasashen biyu wani babban budi ne da Nijar za ta amfana da shi.