1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Italiya ta karbi jirgin ruwan 'yan gudun hijira

Gazali Abdou Tasawa
June 26, 2018

Mahukuntan Italiya sun bai wa jirgin ruwan kasar Danemark dauke da 'yan gudun hijira 108 izinin sauke su a tashar ruwan tsibirin Sisiliya

https://p.dw.com/p/30Hc5
Mittelmeer NGO Mission Lifeline Schiff Flüchtlinge
Hoto: picture-alliance/AP Photo/H. Poschmann

Wani jirgin ruwan dakwan kaya na kasar Danmark dauke da 'yan gudun hijira 108 wadanda aka ceto a ranar Juma'ar da ta gabata a gabar ruwan Libiya ya samu izinin shiga tashar ruwan tsibirin Sicily na kasar Italiya a cikin daren Litinin washe garin wannan Talata bayan da ya share kwanaki uku a gaban tashar jiragen ruwan yana jiran samun izinin shiga.. 

Sai dai kuma ya zuwa yanzu mahukuntan kasar ta Italiya sun ki bayar da izinin shigowa tashar jiragen ruwan ga wani jirgin ruwan na daban na wata Kungiya mai zaman kanta ta kasar Jamus wanda ke can yana gantali a saman teku dauke da wasu 'yan gudun hijirar 234 da ya ceto daga teku. 

Matsalar kwarar 'yan gudun hijira masu kokarin shiga Turai ta tekun Baharum na ci gaba da kara kamari inda a ranar Lahadin da ta gabata kadai aka ceto 'yan gudun hijira kusan dubu daya a gabar ruwan kasar Libiya.