Italiya ta kama masu fasakwabrin bakin haure | Labarai | DW | 18.08.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Italiya ta kama masu fasakwabrin bakin haure

Gwamnatin Italiya ta kama mutane takwas bisa fasakwabrin bakin haure da suka hallaka a tekun Bahar Rum

A wannan Talata mahukuntan kasar Italiya sun bayyana kama mutane takwas da ake zargi da hannu wajen fasakwabrin bakin haure, abin da ya janyo mutuwar kusan mutane 50, lokacin da jirgin ruwa ya nutse a karshen makon da ya wuce.

Wadanda aka kama sun hada da 'yan Moroko uku, da 'yan Libiya hudu gami da matukin jirgin ruwan da ya kife. Fiye da mutane 2,300 suka bakunci lahiya cikin wannan shekara a kokarin shiga nahiyar Turai ta tekun Bahar Rum galibi daga kasashen Afirka da yankin Gabas ta Tsakiya.