1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Italiya ta hana yan cirani fita daga jirgi

Abdullahi Tanko Bala
July 28, 2019

Mahukuntan taliya sun kyale jirgin ruwan da ya dauko yan gudun hijirar da aka ceto akan teku ya tsaya a tashar ruwan Sicily sai dai ba za a bar fasinjojin su sauka ba sai an sami kasar da za ta karbe su

https://p.dw.com/p/3MrIS
Italien Küstenwache
Hoto: Getty Images/AFP/M. Mirabelli

Hukumomin Italiya sun kyale jirgin ruwan dogaran tsaron gabar ruwa na kasar wanda ya dauko yan gudun hijirar da aka ceto a tekun Baharmaliya ya tsaya a tashar jiragen ruwa na Sicily sai dai ba za a bar fasinjojin su sauka ba har sai hukumomi a Brussels sun yanke shawarar kasashen da za su karbi yan gudun hijirar a cewar ministan sufuri na Italiyar Danilo Toninelli a wannan Lahadin.

Yace kungiyar tarayyar Turai ce za ta fadi yadda za a yi saboda batun 'yan gduun hijira batu ne da ya addabi kowa.

Kalamansa sun jaddada matsayin ministan cikin gidan Italiyar Matteo Salvini mai ra'ayin rikau wanda tun farko yace ba za su bar jirgin ya sauke 'yan gudun hijirar a cikin kasar ba har sai sauran kasashen Turai sun bada kudirin karbar 'yan gudun hijirar tukunna.