1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Daruruwan 'Yan gudun hijirar sun sami mafaka a Italiya

Ramatu Garba Baba
July 16, 2018

Gwamnatin Italiya ta amince da bai wa daruruwan 'yan gudun hijira da suka fito daga Afirka mafaka bayan da ta sami amincewar kungiyar kasashen Turai ta EU kan rarraba su a tsakanin sauran kasashe mambobinta.

https://p.dw.com/p/31XGt
Frontext Schiffe Migration Asyl Mittelmeer
Hoto: Imago

Lamarin ya kawo karshen halin wahalar da daruruwan 'yan gudun hijirar suka tsinci kansu a kwanakin da suka kwashe suna zaune cikin kwalekwale a gabar ruwan kasar bayan da suka baro kasashensu na asali.

Kasashen mambobi a kungiyar EU sun amince da su karbi fiye da rabin 'yan gudun hijirar,  a yunkurin dinke barakar da aka samu a tsakanin kasashen na mayar da wadannan mutanen Afirka. Dokar kasa da kasa, ta haramta mayar da 'yan gudun hijirar da suka tsere daga rigingimu masu hadari ga rayuwarsu kasashensu na asali.