Italiya na ganawa ′yan gudun hijira azaba | Labarai | DW | 03.11.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Italiya na ganawa 'yan gudun hijira azaba

Kungiyar Amnesty International ta zargi jami'an 'yan sandar Italiya da gana wa 'yan gudun hijira azaba lokacin yi masu rijista

Kungiyar mai fafutukar kare hakkin jama'a ta zargi jami'an 'yan sandar kasar Italiya da ganawa 'yan gudun hijira azaba a lokacin gudanar da aikin yi masu rijista.

 

Ta yi wannan zargi ne a cikin wani rahoto da ta wallafa a wannan Alhamis, inda ta kuma dora alhakin afkuwar wannan lamari ga Kungiyar Tarayyar Turai wacce ita ce a cewar Amnesty ta matsa wa kasar Italiyar kaimi kan ta tsaurara matakai kan 'yan gudun hijirar masu kokarin shigowa Turai, inda da dama ke kin amincewa a yi rijistansu a kasar ta Italiya a bukatarsu ta zuwa wata kasar ta daban ta Turan domin samun rijistan.

 

Kungiyar ta Amnesty ta ce daga cikin 'yan gudun hijira 170 da ta tattauna da su a lokacin binciken nata, 15 sun yi korafin an yi masu duka ko kuma dosana masu sandar kokara mai lantarki, wasunsu ma har kan al'aura. Tuni ma dai Amnesty ta bukaci da a gudanar da bincike na musamman kan wannan lamari.