Italiya: Girgizar kasa ta lakume rayuka | Siyasa | DW | 25.08.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Italiya: Girgizar kasa ta lakume rayuka

A Italiya adadin mutanen da suka hallaka sakamakon girgizar kasar da ta afku ya kai sama da mutane 240, inda ake ci gaba da tonar burakuzan gine-ginen da suka fadi da fatan samo wadanda ke da sauran numfashi.

Girgizar kasa a Italiya, ana ci gaba da tono gawarwaki

Girgizar kasa a Italiya, ana ci gaba da tono gawarwaki

Motocin asibiti da na kwana-kwana na ci gaba da kai kawo a wuraren da ake ayyukan ceto da fatan gano wadanda ke da asauran numfashi da kuma gawarwaki a karkashin gine-ginen da suka rushe sakamakon girgizar kasar. Kawo yanzu dai mahukuntan kasar ta Italiya sun tabbatar da mutuwar mutane 247, sai dai adadin ka iya karuwa. Daruruwan ma'aikatan ceto dai sun raba dare suna tonar burakuzan gidajen da suka ruguje, inda wani jami'in 'yan kwana-kwana ya ce cikin ikon Allah ana ci gaba da tono wasu mutanen da sauran numfashi.

Barna a yankunan tsaunuka

Kauyukan da ke a yankunan da ke da tsaunuka na arewacin kasar ne dai barnar ta fi kamari, inda a kauyen Amatrice kadai aka samu mutane sama da 200 da suka rasu, kauyen da ana iya cewa ya kusan shafewa daga doran kasa. Rahotanni sun nunar da cewa an kuma samu girgizar kasar kadan-kdan akalla sau 150 a cikin kasa da sa'o'i 12 bayan girgizar kasar ta farko.

Masu aikin ceto na da fatan samo wasu da sauran numfashi

Masu aikin ceto na da fatan samo wasu da sauran numfashi

Dubunnan iyalai ne dama 'yan yawon bude ido suka rasa muhallansu kuma da dama daga cikinsu sun samu mafaka a wasu manyan sansanoni na musamman da aka bude, a yankunan da girgizar kasar ba ta shafa ba. A wani jawabi da ya yi a loakcin wani taron gaggawa da ya kira tare da hukumomin agaji da mahukuntan yankuna da girgizar kasar ta shafa, Firaministan Italiyan Matteo Renzi ya yi kira ga 'yan kasarsa su kasance masu taimakon juna a cikin wannan yanayi da aka shiga.

Bukatar taimakon kai da kai.

Ya ce: "Wannan lokaci ne da ya kamata mu hada kanmu wuri guda da tausayawa juna, mu kuma dukufa ga yin addu'o'i. Lokaci ne da ya kamata al'ummar Italiya baki daya mu rungumi juna. Mu yi watsi da duk wani cece-kuce da muka saba yi kan wasu manufofi na siyasa mu kasance tsintsiya madaurinki daya. Ya kamata mu jinjina wa jami'an kwana-kwana da sojoji da jami'an agaji dangane da rawar da suke takawa cikin aikin ceto a yanzu."

Firaministan Italiya Matteo Renzi ya nemi al'umma su hada kai su taimaki juna

Firaministan Italiya Matteo Renzi ya nemi al'umma su hada kai su taimaki juna

Firaministan kasar ta Italiya matteo Renzi ya kuma yi kiran wani taron gaggawa na majalisar ministocinsa domin tattauna matakan agajin da ya kamata a samar wa yankunan da lamarin girgizar kasar ya shafa. Kasashen duniya dai na ci gaba da aika sakon ta'aziyya da kuma jaje ga mahukuntan kasar ta Italiya bisa wannan iftala'in da ya afka musu. Sai dai kuma kwararru a fannin ayyukan ceto dama masana ilimin girgizar kasa, sun nuna rashin jin dadinsu dangane da yadda aka wayi gari kasar ta Italiya ba ta mallaki wadatattun kayan rigakafin afkuwar irin wannan hadari ba, duk kuwa da cewa hukumomi sun san kasar na daga cikin jerin kasashen duniya masu hadarin fuskantar girgizar kasa a ko yaushe.

Sauti da bidiyo akan labarin