Issac Yacouba Zida ya zama shugaban Burkina Faso
November 1, 2014Talla
Sojojin kasar Burkina Faso sun amince da zaben Laftanan Kanar Isaac Yacouba Zida a matsayin sabon shugaban kasar da zai jagoranci wannan kasa na rikon kwarya, bayan murabus din da shugaba Blaise Campaore yayi, wanda yanzu haka yake gudun hijira a birnin Yamouskro na kasar Cote d'Ivoir. A wata sanarwa da rundunar sojan kasar ta Burkina faso ta fitar a dazu-dazun nan bayan kammala wani zaman taro na manyan sojojin kasar a birnin Wagadugu, sun tabbatar cewa ga baki dayan su sun amince da Kanar Issac Zida a matsayin sabon shugaban kasar na rikon kwarya, inda babban hafsan hafsoshin kasar Janar Nabere Honore Traore ne ya sa hannu ga sanarwar.