1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Israila ta soki binciken FBI kan Abu Akleh

Abdullahi Tanko Bala
November 15, 2022

Ministan tsaron Israila Benny Gantz ya ce binciken Amirka kan kisan Shireen Abu Akleh kuskure ne kuma Israila ba za ta bada hadin kai ga wani bincike daga waje ba.

https://p.dw.com/p/4JYpy
West Bank - Wandbild, das die ermordete palästinensisch-amerikanische Journalistin Shireen Abu Akleh darstellt
Hoto: Mahmoud Illean/AP

Israila ta ce binciken da hukumar FBI ta Amirka tace za ta yi kan kisan Ba Amurkiya kuma 'yar asalin Falasdinu Shireen Abu Akleh kuskure ne kuma Israila ba za ta bada hadin kai ga binciken ba.

Abu Akleh 'yar jaridar Aljazeera ta rasa ranta ne yayin da ta ke daukar rahotoanni yayin wani farmaki da sojojin Israila suka kai yankin gabar yamma a ranar 11 ga watan Mayu.

A ranar 5  ga watan Satumba Israila ta amince cewa akwai yiwuwar daya daga cikin sojojinta ya harbi Abu Akleh bisa kuskure. Ministan tsaron na Israila Benny Gantz yace Israila ba za ta bada hadin kai ga wani bincike daga waje ba.

Iyalan 'yar jaridar ta Aljazeera Shireen Abu Akleh a wata sanarwa da suka fitar sun yabawa matakin Amirka na binciken musababbin kisanta wanda suka ce suna fatan samun bincike na adalci.