1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tsagaita wuta ta fara aiki a Gaza

Abdullahi Tanko Bala
November 14, 2019

Kungiyar Jihad al Islami a Gaza ta sanar da tsagaita wuta a wannan Alhamis bayan Israila ta baiyana kawo karshen farmaki a yankin.

https://p.dw.com/p/3T3Fa
Israel Palästina Iron Dome fängt Rakete aus Gaza ab
Hoto: Reuters/A. Cohen

Wani mai magana da yawun rundunar sojin Israila ya tabbatar da tsagaita wuta tsakanin sojojin da mayakan Jihadil Islami a zirin Gaza a wannan Alhamis bayan shafe tsawon sa'oi 48 ana tashe tashen hankula.

Laftanar kanar Avichy Adraee na runudunar sojin Israilan a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter yace duk da haka Israila za ta gasa wa kungiyar 'yan gwagwarmayar Jihadin aya a hannu.

Shi ma ministan harkokin wajen kasar Israel Katz yace sojin Israila za su mayar da martani daidai gwargwado idan aka kai musu hari yana mai cewa Israila ba za ta saurara wa hari daga Gaza ko kuma wani wuri ba.

Kakakin kungiyar Jihadil Islami Musab al Berim shine ya sanar tsagaita wutar wadda kasar Masar ta shiga tsakani