1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Israila ta hana wasu Amirkawa shiga kasarta

Binta Aliyu Zurmi
August 16, 2019

Hukumomi a kasar Israila sun haramtawa wasu mata biyu 'yan majalisar dokokin Amirka na jam'iyyar Democrats shiga kasar a shirin wata ziyara da za su kai,

https://p.dw.com/p/3Nyw3
Ilhan Omar und Rashida Tlaib
Hoto: picture-alliance/AP Photo/J. S. Applewhite

Tun bayan sanarwar da Israila ta fitar na hana matan biyu yan majalisar dokoki na jam'iyyar Democrats, shugaba Trump ya yi maraba da matakin yana mai cewar da ya kasance babban rauni idan da Israila ta bar matan su shiga cikin kasarsu. Ya kara da cewa matan basa kaunar kasar Israila da ma al'ummar Yahudawa. Trump ya soki lamirin matan inda ya ce sun kasance abin kunya  ga kasar.

Wannan mataki na haramtawa 'yar majalisa Rashida Tlaib da 'yar majalisa Ilham Omar ziyartar abokan huldar kasar Amirka mataki ne da ba'a taba gani ba kuma babbar alama ce da ta shafi siyasar kasashen biyu.