Isra′ila ta amunce da matakin tsagaita wuta | Labarai | DW | 21.11.2012
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Isra'ila ta amunce da matakin tsagaita wuta

Bayan kai ruwa rana,Hillary Clinto ce ta karanta sanarwar tsagaita wuta tsakanin Isra'ila da Hamas daga birnin Alkahiran Masar.

Bisa ga dukkan alamu hakar masu shiga tsakani a rikicin da ya barke da Isra'ila da mayakan Palastinawan yankin Gaza,ta cimma ruwa,bayan da hukumomin Istra'ila suka amunce da shawarar da aka bada ta tsagaita wuta tsaklanin kasar da mayakan Hamas na Gaza. A cewar gidan talabijan kasar ta Isra'ila,Hillary Clinton ce daga birnin Alkahiran Masar ta bayana wannan sanarwar ,matakin da zai fara aiki karfe tara agogon GMT.
To saidai duk da wannan sanarwar hukumomin na Isra'ila sunce ba za su dage takunkumin da suka lakabawa yankin na Gaza ba inda ake safarar makamai. To saidai kawo yanzu hukumomin Hamas basu ce komai a dangane da sanarwar.

Mawallafi: Issoufou Mamane
Edita: Usman Shehu Usman