Isra´ila ba zata mutunta tayin tsagaita wuta da ´yan takifen Falasdinawa ba | Labarai | DW | 24.11.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Isra´ila ba zata mutunta tayin tsagaita wuta da ´yan takifen Falasdinawa ba

Isra´ila ta yi watsi da tayin tsagaita wuta da kungiyoyin sojin sa kai na Falasdinawa suka yi mata. Mai magana da yawun gwamnatin Isra´ila ta ce ba za´a amince da tayin domin ya tanadi dakatar da harba rokoki ne kadai daga Zirin Gaza zuwa cikin Isra´ila. Kakakin ta ce Isra´ila zata daina farmakin sojin kadai idan sojojin sa kan Falasdinawa suka ajiye makansu. Da farko kungiyoyin na Falasdinawa sun bukaci Isra´ila ta kawo karshen matakan sojin da take dauka a Zirin Gaza da Gabar yamacin kogin Jordan. Fatah da Jihadin Islami na daga cikin kungiyoyin Falasdinawa masu gwagwarmaya da suka yi wannan tayi. A kuma can arewacin Gaza sojojin Isra´ila sun harbe wani dan kungiyar Hamas da kuma wani yaro dan shekaru 10 har lahira.