1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iritiriya ta shiga yakin Tigray na Habasha

Zainab Mohammed Abubakar ZUD
September 30, 2022

Matakin na ci gaba da kara ruruta wutar rikicin yankin Tigray na Habasha da aka fara tun shekara ta 2020.

https://p.dw.com/p/4HaOP
Shugaban Iritiriya Isaias Afwerki yayin bude ofishin jakadancin kasarsa a Habasha
Shugaban Iritiriya Isaias Afwerki yayin bude ofishin jakadancin kasarsa a HabashaHoto: Fitsum Arega/Prime Minister Office Ethiopia

Tsohon sabani, sabbin hanyoyin zalunci, wannan shi ne taken labarin da Jaridar Süddeutsche Zeitung kan rikicin Tigray. Jaridar ta ce shugaban kasar Iritiriya  Isaias Afewerki ya sake mamaye yankin Tigray na kasar Habasha. Ko mene ne dalilin da ya sa shugaban mai salon mulkin kama karya ke taka irin wannan muguwar rawa a tashe-tashen hankula a yankin kusurwar Afirka?

Sai aka samu wani yanayin gangami, ba a birnin Moscow ba, amma a Asmara, da ke Afirka. Isaias Afewerki, shugaban Iritiriya  kuma daya daga cikin masu mulkin kama-karya a Nahiyar, ya karfafa rundunar sojojinsa da sabbin jami'ai. Yanzu haka yana tura su fagen daga a yankin Tigray da ke arewacin Habasha.

A farkon yakin Habasha dai dakarun Iritiriya sun shiga tsakani kafin a ce sun janye. Tsagaita bude wuta dai ya dauki tsawon watanni biyar kacal, kafin fada ya sake barkewa a yankin Arewa maso gabashin wannan kasa ta Afirka mafi girma kuma mai yawan kabilu tun farkon watan Satumba. Kuma a yanzu Iritiriya na shiga tsakani da sojoji, kamar yadda jakadan Amirka a yankin kusurwar Afirka Mike Hammer ya tabbatar, inda ya ce "mun bi diddigin yadda sojojin Iritiriya suka kutsa ta kan iyaka. Sun kasance babbar damuwa kuma muna Allah wadai da su."

Kanar Paul-Henri Damiba na Burkina Faso
Kanar Paul-Henri Damiba na Burkina FasoHoto: Luc Gnago/REUTERS

Ita kuwa jaridar Neues Deutschland sharhi ta yi mai taken "Burkina Faso ta zama wurin ta'addanci

a yankin Sahel, masu tsattsauran ra'ayi na kara karfi duk da kasancewar dakarun Jamus a nan"

Jaridar ta ci gaba da cewa Burkina Faso dai na kara shiga cikin ta'addancin masu tada kayar baya, inda aka kashe mutane 2,224 a hare-hare sama da 900 a watannin shidan farko na wannan shekarar kadai. Rundunar Jamus ta Bundeswehr ta shafe shekaru tana aiki, ba a Mali kadai ba, har ma a duk fadin yankin Sahel.

A kasar Mali, Bundeswehr na cikin shirin bada horo na kungiyar Tarayyar Turai, EUTM, wanda ke aiki daga can a duk kasasahen Sahel biyar da suka hadar da Moritaniya da Mali da Burkina Faso da Nijar da kuma Chadi. A kasar Mali dai, a halin yanzu komai ya dagule game da aikin, saboda Jamus na ganin cewar gwamnatin da ta yi juyin mulki ba aminiyar da za a dogara da ita ba ce.

Yanzu hankali ya koma kan Nijar a matsayin muhimmiyar kasa da ake bi ta cikinta zuwa Turai ta barauniyar hanya. Burkina Faso na ci gaba da kasancewa a gefe duk da karuwar rashin zaman lafiya. A can ma, Sojoji ne ke rike da madafan iko tun bayan juyin mulkin watan Janairun 2022, kamar yadda aka yi a Mali. Kuma ana ci gaba da kai hare hare a sassa dabam-dabam na gidan.

Shugaba Emmerson Dambudzo Mnangagwa na Zimbabuwe
Shugaba Emmerson Dambudzo Mnangagwa na ZimbabuweHoto: Dominika Zarzycka/NurPhoto/picture alliance

Yanzu kuma sai Zimbabuwe, inda jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta yi tsokaci game da yadda ake gasawa masu sukar gwamnatin kasar aya a hannu tare da gurfanar da su a gaban kuliya.

Ba za a rasa motar 'yan sanda ta musamman a gefen titin a kullum ba. Lokacin da Douglas Coltart ya karbi wasu abokan hulda a Harare, ya tabbatar da cewar idanun 'yan sanda na kanshi. Lauyan kare hakkin dan Adam na Zimbabwe ya ce "A kullum muna aiki ne bisa zaton cewa ana kallon mu." Kamar abokan aikinsa, a kullum yana aiki cikin fargaba.

A Zimbabuwe dai, ba a manta da mulkin Robert Mugabe na shekaru 37 ba. Lokacin da shugaban, wanda ya rikidar da mulkinsa kamar na kama-karya, wanda aka tilasta wa murabus a shekara ta 2017. Sai dai kamar yadda kungiyoyin kare hakkin bil Adama suka bayyana, lamarin ya kara tabarbarewa a karkashin magajin Mugabe watau shugaba Emmerson Mnangagwa.