Iraqi ta nemi a binciki kungiyar OPEC | Labarai | DW | 04.12.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Iraqi ta nemi a binciki kungiyar OPEC

Ministan man Fetur na kasar Iraq Bijan Zanganeh ya bukaci a gudanar da cikakken bincike a kungiyar kasashe masu arzikin man Fetur game da dalilan da suka janyo ficewar kasar Qatar daga kungiyar.

A ranar Litinin din da ta gabata ce dai kasar Qatar ta sanar da shirinta na ficewa daga kungiyar ta OPEC don mayar da hankali a harkar Iskar Gas.