Iran ta fiddo da sabbin fasahar soji | Labarai | DW | 28.11.2012
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Iran ta fiddo da sabbin fasahar soji

Kwamondojin sojan ruwan Iran sun ruwan sun gwada sabbin jiragen ruwa ƙirar cikin gida

Ƙasar Iran ta gudanar wani atisayen sojan ruwa, inda ta fito da wasu jiragen yaƙi na ruwa sabbin dake iya goyon makamai masu linzami da kuma harba daga cikin teku. Kwamondojin sojan ruwan ƙasar ta Iran sun yi layi suna kallo lokacin da ake gwada wani sabbin jirgen yaƙi na ruwa ƙirar cikin gidan ƙasar ta Iran, wanda ke da kariyar daga wani makamin linzami. Ƙasar ta Iran dai a wannan karon ta yi gwajin wasu sabbin jiragen yaƙin ruwa wanda ta ƙera da kanta. Gidan talabijin ɗin gwamnatin ƙasar, ya ruwaito kwamandan sojin ruwan Iran, Rear Admiral Habibollah Sayyari na mai cewa, ya zama wajibi ga ƙasar Iran ta mallaki fasahar zamani ta yaƙi, don kare iyakokinta. Ƙasar Iran a yan shekarunnan ta bada ƙarfi wajen inganta ɓangaren sojan sama da na ruwa, inda tace duk wani hari da za a iya kai mata nan gaba, to mai yiwa a fara ta waɗannan hanyoyin. Don haka suka ɗauki matakan mallakar fasahar zamani ta yaƙin sama da na ƙasa.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Yahouza Sadissou Madobi