1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iraki ta sallami babban kwamandan sojin kasar daga aiki

Binta Aliyu Zurmi
November 28, 2019

Rahotanin da ke fitowa daga Iraki na cewar jami'an tsaro sun harbe mutum 35 daga cikin masu zanga-zanga biyo bayan barkewar rikici a Bagadaza babban birnin kasar. 

https://p.dw.com/p/3TuST
Adil Abdul Mahdi
Hoto: picture-alliance/AP Photo/B. Ozbilici

Jami'an tsaron sun yi amfani da harsasan gaske a kan mutanen, wanda baya ga kisan, sun kuma jikkata wasu sama da mutum dari da hamsin. Tuni ma firaministan kasar Adel Abdel Mahadi ya sallami babban kwamandan sojin kasar daga aiki sakamakon kisan da dakarunsa suka yi wa masu zanga-zangar. Ya zuwa yanzu an kara yawan jami'an tsaron a kan tituna a kokari na yayyafa wa rikicin ruwa.