Iraki ta ayyana samun nasara kan IS | Labarai | DW | 10.12.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Iraki ta ayyana samun nasara kan IS

Gwamnatin Iraki ta ayyana yin nasara baki daya kan Kungiyar IS wacce a shekara ta 2014 ta kwace iko da kashi daya daga cikin uku na kasar.

Gwamnatin Iraki ta ayyana yin nasara baki daya kan kungiyar IS wacce a shekara ta 2014 ta kwace iko da kashi daya daga cikin uku na kasar. Firaministan kasar Haidar Al- Abadi  ne ya yi wannan ikrari a wani jawabi da ya gabatar ga 'yan kasar a jiya Asabar a gaban ministan tsaro da kuma shugabannin sojojin kasar.

 
Sai dai Firaminista Abadi ya ce duk da nasarar da suka yi ta karya lagon Kungiyar ta IS baki daya, za su ci gaba da zaman a ko yaushe cikin shirin ta kwana. 

Firaminista Al-Abadi ya kara da cewa a yanzu sabon yakin da za su sa a gabansu shi ne na cin hanci wanda ya ce shi ne babbar matsalar da ke kawo cikas ga cigaban kasar. Gwamnatin kasar ta Iraki ta ayyana wannan rana ta Lahadi a matsayin ranar hutu domin raya ranar nasarar da kasar ta samu kan kungiyar IS.