Interpol ta tura kwararru Sri Lanka don bincike bayan harin ta′addanci | Labarai | DW | 22.04.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Interpol ta tura kwararru Sri Lanka don bincike bayan harin ta'addanci

Tawagar masana ta hukumar 'yan sandan kasa da kasa za ta gudanar da bincike a kasar Sri Lanka biyo bayan hare-haren kan coci-coci da otel-otel lokacin bikin Easter.

Hukumar 'yan sandan kasa da kasa wato Interpol ta tura tawagar masana binciken kwakwaf kasar Sri Lanka a daidai lokacin da kasar ke juyayin hare-haren da suka yi sanadiyyar rasa rayukan mutane da yawansu ya kai 290 a guraren ibadun mabiya addinin Kirista da kuma otel-otel na saukar baki.

Tun da farko mahukuntan kasar ta Sri Lanka sun bukaci Interpol ta taimaka musu wajen binciken mummunan harin da ya gudana a lokacin bikin Easter kamar yadda hukumar ta shaida wa manema labarai a wannan Litinin din.

Tawagar masanan wacce ta kunshi wadanda suka yi fice a binciken bama-bamai da gano masu laifi don lalubo duk wadanda ke da hannu a wannan hari ta baza koma a kafafen sadarwar zamani tare da gayyatar duk wanda ke da masaniya game da harin.

Yanzu haka dai mahukuntan kasar sun kafa doka ta-baci da ta ba wa 'yan sanda da sojoji karin iko na tsare da kuma binciken wadanda ake zargi ba tare da jiran umarni daga kotu ba.