1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Inganta rayuwar al'umma ne tushen dangantakar Amirka da Jamus

June 19, 2013

Shugaba Obama ya bukaci Turai ta sake fasalin manufofin tattalin arzikinta domin warware matsalar rashin aikin yi a nahiyar.

https://p.dw.com/p/18tC2
US President Barack Obama (L) meets German Chancellor Angela Merkel (R) on June 19, 2013 at the Chancellery in Berlin. Barack Obama will walk in John F. Kennedy's footsteps this week on his first visit to Berlin as US president, but encounter a more powerful and sceptical Germany in talks on trade and secret surveillance practices. AFP PHOTO / JOHANNES EISELE (Photo credit should read JOHANNES EISELE/AFP/Getty Images)
Hoto: Johannes Eisele/AFP/Getty Images

Shugaban na Amirka Barak Obama, wanda ya gana da manyan jami'an gwamnatin Jamus ciki harda shugabar gwamnati Angela Merkel a lokacin ziyarar ta sa a birnin na Berlin, ya yi gargadin cewar, ko da shike yana da yakinin cewar shugabannin gamayyar kasashen Turai da ke yin anfani da takardar kudi ta Euro za su iya shawo kan matsalar bashin kudin da ke addabar wasu kasashen, amma bai kamata manufofin da suka shafi matakan tsuke bakin aljihu da kuma sauye-sauyen tattalin arzikin da suke dauka yasa masu tsara manufofi a nahiyar su mance da burin da ke gabansu na inganta rayuwar al'umma ba.

Magabatan biyu sun kuma tattauna batun kammala yarjejeniyar da ta shafi gudanar da harkokin kasuwanci a tsakanin Turai da Amirka ba tare da wani shinge ba, yarjejeniyar da kuma shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta tabbatar wa bakon nata da cikakken goyon bayan kasarta:

" Shika-shikan dokokinmu na tabbatar da walwala a rayuwa sun tanadi taimakawa dan adama ya gaskata da kansa. shi ya sa mu ke da tambaya dangane da batun daidaito, da batun hanyoyin dangantaka wato abubuwan da za mu iya mu ci gaba da tattaunawa a kai, da wuraren da zamu iya kulla yarjejeniyar musayar bayanai tsakanin ma'aikatanmu, tsakanin jami'an ma'aikatar cikin gida na nan Jamus da kuma ma'aikatan Amirka kamar yadda aka alkawarta, idan dai a ka cimma matsaya kan wadannan batutuwa ina tsammanin za'a cigaba da wannan tattaunawa yadda ya kamata ."

U.S. President Barack Obama and his German counterpart Joachim Gauck (R) wave as they meet at the presidential residence Bellevue Castle in Berlin, June 19, 2013. Obama will unveil plans for a sharp reduction in nuclear warheads in a landmark speech at the Brandenburg Gate on Wednesday that comes 50 years after John F. Kennedy declared "Ich bin ein Berliner" in a defiant Cold War address. REUTERS/Fabrizio Bensch (GERMANY - Tags: POLITICS)
Shugaba Obama da shugaban Jamus, Joachim GauckHoto: Reuters

Wani batun da Merkel da Obama suka tabo a tattaunawar da suka yi a Berlin dai ya shafi batun daukar matakan warware rikicin Siriya da kuma irin rawar da kasashen biyu ke takawa a rikicin kasar Afghanistan, wanda shugaban Amirka ya yaba da irin gudummowar da Jamus ke bayar wa ta wannan fannin.

Sai dai kasancewar ziyarar ta shugaban na Amirka ta zo ne a dai dai lokacin da ake ta cece-kuce game da bayanan da suka fito fili a baya bayannan dangane da sauraron bayanan sirrin jama'a ta hanyar yanar gizo da kuma wayoyinsu, wanda kuma hatta gwamnatocin Turai suka nuna rashin jin dadinsu ga halayyar Amirkar, shugaba Obama ya ce da kyakkyawar manufa ce hukumomin leken asirin Amirka ke daukar matakan:

Ya ce " Abin da zan shaida wa kowa da kowa anan Jamus da kuma a sauran sassa na duniya shi ne cewar, hakan din takaitacce ne kuma ya shafi bayanan da aka tsegunta mana game da batutuwan da suka shafi ta'addanci da kuma yaduwar makaman kare dangi."

Bundesaußenminister Guido Westerwelle (FDP) wartet am 12.06.2013 auf den beginn der Sitzung des Bundeskabinetts im Bundeskanzleramt in Berlin. Foto: Kay Nietfeld/dpa +++(c) dpa - Bildfunk+++
Ministan harkokin wajen Jamus, Guido WesterwelleHoto: picture-alliance/dpa

Da ya ke tsokaci dangane da takaddamar da ta kunno kai a tsakanin Jamus da Amirka a kan batun na sauraron sirrin jama'a, ministan harkokin wajen Jamus Guido Westerwelle cewa yayi ai dama akan saba a tsakanin abokai :

Ya ce " Kawance da ke tsakanin Jamus da Amirka mai zurfi ne wanda ba za mu iya kawar da samun sabani ba. Akan haka ne nake bada shawarar cewar bai kamata mu mayar da hankali akan banbancin ra'ayin da muke da shi kawai ba a lokacin wannan ziyarar da ke cike da tarihi."

Wani batun da shugaban Amirka ya tabo a lokacin ziyarasa a birnin na Berlin kuwa shi ne alkawarta cewar zai kara yin hubbasa wajen shawo kan matsalar hayaki mai gubar da masana'antu ke fitar wa a matsayin wani bangare na yaki da sauyin yanayi a duniya.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Zainab Mohammed Abubakar