Ingancin bayanai a kan amfani da guba a Siriya | Labarai | DW | 03.09.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ingancin bayanai a kan amfani da guba a Siriya

Majalisar dokokin Faransa za ta tafka muhawa a kan hujjojin zargin yin amfani da makamai masu guba a Siriya.

Gwamnatin Faransa ta mikawa majalisar dokokin kasar bayanai dangane da zargin Siriya da kaddamar da hare hare da makamai masu guba. A cewar rahoton na wannan Litinin, gwamnatin shugaba Assad ce ta kai hare haren a watan jiya domin fatattakar 'yan tawayen da ke wajen Damascus, babban birnin kasar. A wanna Larabar ce (03.09.13), majalisar dokokin kasar ta Faransa za ta tafka muhawara a kan batun. A karkashin tsarin mulkin Faransa dai, shugaba Francois Hollande , baya bukatar amincewar majalisar dokoki gabanin kaddamar da hari, kuma shugaban, bai nuna wata alamar neman majalisar ta jefa kuri'a a kan batun ba.

Dama a makon jiya ne majalisar dokokin Birtaniya ta jefa kuri'ar yin watsi da batun daukar matakin soji a Siriya, a wani abin da ke zama gagarumar koma baya ce ga kawayenta na kasashen yammacin duniya..

Can a kasar Amirka kuwa, gwamnatin shugaba Obama ce ta mika batun rikicin na Siriya ga majalisar dokoki, domin shiga tsakani, amma kuma 'yan majalisar dokokin na dari-dari game da batun. Senata John McCain, ya bayyana cewar, idan har majalisar dokokin ta jefa kuri'ar yin watsi da daukar matakin soji a Siriya, to, kuwa hakan zai zubar da mutuncin Amirka:

Ya ce " Idan har majalisar dokoki za ta yi watsi da kudiri - irin wannan, bayan da shugaban kasa ya mikashi gareta, to, kuwa sakamakonsa zai kasance mai hatsarin gaske, domin kuwa mutuncin wannan kasar zai zube a idanun kawayenta da makiyanta baki daya."

Majalisar dokokin dai za ta jefa kuri'a ne bayan dawowarta daga hutu.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Abdourahamane Hassane