INEC ta sanar da bayanai kan zabukan Najeriya | Siyasa | DW | 20.03.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

INEC ta sanar da bayanai kan zabukan Najeriya

Hukumar zaben Najeriya ta bayyana sabbin matakan da ya kamata masu kada kuri'u su bi don kaucewa kura-kurai lokacin zabe

A yayinda ya rage mako guda a gudanar da zabuka a Najeriya, hukumar zaben kasar ta yi bayayana sabbin tsare-tsare da matakan da masu jefa kuri'a zasu bi musamman batun kunshi ga mata saboda amfani da naurara tanatance masu jefa kuri'a.

Hukumar dai ta bayyana sabbin tsare-tsaren ne musamman tsarin akwatin jefa kuri'a da a wannan lokacin ta ce za ta yi amfani da akwatuna guda uku ne ga zabubbuka uku da za'a yi a ranar 28 ga watan nan, maimakkon guda daya da aka saba amfani da shi ga zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisar datawa da na wakilai.

Mataimakin darakta mai kula da hulda da jama'a na hukumar zaben Mr Nick Dazzan, ya ce sauyin tsarin an yi shi ne saboda saukaka kidayar kuru'u da ma kaucewa duk wata kumbiya-kumbiya a wajen jefa kuri'a.

‘'Na takarar shugaban kasa akwai akwati na musamman wanda za'a kada kuri'a a ciki, marufinsa ja ne haka nan takaradar jefa kuri'a ma ja ne, sa'annan kuma na majalisar dattawa shi kuma launin murfinsa baki ne sannan takaradar kuri'a baka ce. Sai na 'yan majalisar dattawa murfinsa kore ne, takaradar jefa kuria ita ma koriya ce''

Ko ina aka kwana ga batun kuru'in da za'a jefa su bisa kuskure a akwatin da ba nasu ba, wanda a baya hukumar ta ce shikenan an yi asararsu? Har illa yau ga Mr Nick Dazan.

‘'An yi nazari a kan wannan an duba wahalara da mai jefa kuri'a xzai sha a ranara zabe, koda a cikin rububi mutum ya jefa kuri'a a cikin akwatin da bai dace ba, to kafin a sanar da sakamakon zabe a cibiyar za'a tabbatar da cewa an ware wadannan kuru'un daha na shugaban kasa da na dan majalisar datawa da ma na wakilai duka daban-daban''.

Sauti da bidiyo akan labarin