1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

INEC ta dauki matakin rage yawan jam'iyyu a Najeriya

December 26, 2012

Ya zuwa yanzu hukumar zabe a Najeriya ta bayyana soke jerin jam'iyyu har 31 sannan kuma ta na shirin kara yawan 'yan barzahun a wani kokarin tabbatar da tsabta a cikin tsarin zaben kasar.

https://p.dw.com/p/179Cu
Hoto: AP

A baya dai an sha gwaji ana sauyawa, an kai ga kusan 60 kafin aka dawo wa biyar sannan kuma sai biyu duk dai a kokarin tarrayar Nijeriya na ginin jam'iyyun siyasa a kasar.

Duk da cewar dai fagen siyasar ya fuskanci sake haihuwar wasu kwaya uku bayan kawo karshen mulkin sojan kasar wani hukuncin kotun kolin kasar ya tilasta rijistar karin jam'iyyu ya zuwa 65 a lokutan zabukan tarrayar da suka gabata.

To sai dai kuma a yanzu haka kasar na shirin koma gidan jiya sakamakon matakin hukumar zaben mai zaman kanta a Najeriya wato INEC na rage yawan jam'iyyun dake taka rawa cikin fagen siyasar kasar.

Matakin na da dalilai na shirya tsabtataccen zabe

Ya zuwa yanzu dai hukumar ta bayyana soke jerin jam'iyyu har 31 sannan kuma ta bayyana aniyar kara yawan 'yan barzahun a wani abun da ta kira kokarin tabbatar da tsabta a cikin tsarin zaben kasar ta Najeriya.

To sai dai kuma maimakon tsabtar, matakin INEC din yanzu haka tuni ya kama hanyar jawo kace nace da musayar yawu a tsakanin al'ummar kasar dake masa kallon wani kokari na zagon kasa ga demokradiyyar kasar.

Wahlen Nigeria Genral Muhammadu Buhari
Janar Muhammadu Buhari mai ritayaHoto: AP

Jam'iyun da suka sha kuradar hukumar INEC din dai sun nufi kotu domin ja da hukuncin da suka ce ya saba da hankali da ma kundin tsarin mulkin tarrayar Najeriya.

Akwai dai zargin kokarin hukumar na sake mai da tarrayar ta Najeriya ya zuwa tsarin jamhuriya ta biyu mai jam'iyyu biyar kacal abun kuma da a cewar Mallam Faruk BB Faruk dake zaman masanin harkokin siyasa ba zai haifarwa da kasar da mai ido ba.

Dilancin kananan jam'iyyu

Babban zargi dai a cewar hukumar INEC na zaman komawar kananan jam'iyyun kasar zuwa kafa ta kasuwanci a tsakanin shugabbaninsu da a wasu jam'iyun ma ya kai ga mai da su jam'iyyu a jaka ga mai saye.

A baya dai manyan jam'iyyun kasar sun rika amfani da kananan wajen kokarin halasta magudin zabe kama daga na shi kansa shugaban kasar ya zuwa gwamnoni da ragowar mukamai na siyasa.

Parlamentswahl in Nigeria
INEC kan dauki masu yi wa kasa hidima aiki a lokacin zabukan NajeriyaHoto: AP

Banda kuma kudaden da ake zargin jam'iyyun daga karba daga INEC ba kuma tare da nuna yadda suke batar da su a bainar jama'a ba.

Jerin zarge zargen kuma da a cewar Mallam Yunusa Tanko dake zaman sakataren jam'iyar NCP dake zaman daya daga cikin kananan jam'iyyun dake fuskantar barazanar zuwa barzahun zancen banza ne

Abun jira a gani dai na zaman tasirin sabon matakin INEC din ga siyasar tarrayar Najeriya da ta sha fuskantar sama da kasa da kuma ke fama da matsala ta rashin akida a tsakanin masu sana'arta.

Mawallafi: Ubale Musa
Edita: Mohammad Nasiru Awal