Indonesiya ta gano gawarwakin mutane 54 | Labarai | DW | 18.08.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Indonesiya ta gano gawarwakin mutane 54

An gano gawarwakin mutane 54 da suka mutu a hadarin jirgin Trigana Air Service na kasar da ya fadi ran Lahadi .

Ma'aikatan ceto na kasar Indunusiya sun bada sanarwar gano a wannan Laraba gawarwakin mutane 54 da suka mutu a cikin hadarin jirgin saman kamfanin Trigana Air Service na kasar na ranar Lahadin da ta gabata . Hukumomin kasar sun bayyana cewa sun gano kuma tarkacen jirgin wanda ya yi day-day a yayin da wani sashensa ya kone kurmus. Sun kuma ce jirgin ya fadi ne a cikin wasu tsaunika masu kuma rukukin itatuwa da ke da wuyar shiga . Abun da ke kawo cikas a kokarin da ake na kwashe illahirin gawarwakin.

Haka zalika sun ce suna ci gaba da neman na'urar nadar bayanai ta jirgin domin sanin takamaiman abunda ya haddasa hadarin. A ranar Lahadin da ta gabata ne dai jirgin saman kamfanin Trigana Air Service wanda ke aikin jigilar fasinja a tsakanin biranen kasar ya fadi da mutane 54 a cikinsa.

Wannan dai shine karo na ukku a cikin shekara daya da ake samun hadarin jirgin sama a wannan kasa wacce ta yi kaurin suna wajan rashin ingancin jiragen sama da ke sufurin al'umma a kasar