Indonesiya: Gobara ta halaka rayuka | Labarai | DW | 26.10.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Indonesiya: Gobara ta halaka rayuka

Rahotanni daga kasar Indonesiya na cewa akalla mutane 46 ne suka mutu sakamakon tashin wata gobara a wani kamfani na sarrafa kayan wasan wuta da ake amfani da su yayin bukukuwa.

Indonesien Brand in Feuerwerkfabrik in Tangerang (picture-alliance/AP Photo/T. Syuflana)

Kamfanin da ya yi gobarar da ta hallaka mutane sama da 40 a Indonesiya

Da yake magana kan wannan batu, Harry Kurniawan shugaban 'yan sandan birnin Tangerang inda kamfanin yake, ya ce ya zuwa yanzu dai sun gano gawarwakin mutane 46, sannan kuma su na ci gaba da neman wasu mutane 10 a wannan ma'aikata da ke da ma'aikata 103.

Gobarar dai ta tashi ne da wajejen karfe tara na safe agogon kasar, karfe biyu na dare agogon GMT a birnin na Tangerang da ke kusa da Jakarta babban birnin kasar.