Daruruwan mutane sun mutu a Indonesiya
September 29, 2018Talla
Hukumar kula da yanayi ta kasar ta shaidar da cewar wasu mutanen 540 sun jikkata a yankin Palu da ke tsibirin Sulawesi, mai dauke da mutane dubu 350, daura da masu yawon bude ido.
A wannan Asabar din ce dai masu aikin ceto suka sanar da gano karin gawarwakin mutanen da suka rasa rayukansu, a yayin da dubban gidaje da asibitoci da wasu muhimman gine-gine suka rushe sakamakon girgizar kasar.
Bugu da kari rahotanni da ke fitowa daka Indonesiyan na nuni da cewar, ambaliyar ruwa na cigaba da barazana ga daukacin tsibirin, a yayin da aka rufe babbar hanyar zuwa Palu saboda zabtarewar kasa.