1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An gano tarin gawakin wasu matasa a Indonesiya

Salissou Boukari
October 2, 2018

Masu ayyukan ceto a yankin tsibirin Celebes na kasar Indonesiya, sun gano wasu gawawakin gwamman matasa a karkashin baraguzzan wata Coci da ta ruguje sakamakon girgirar kasar da ta wakana ta ranar Juma'a.

https://p.dw.com/p/35qfr
Indonesien Palu Massengrab für Tsunami-Opfer
Hoto: DW/Nurdin Amir

Adadin baya-bayan nan da hukumomin yankin suka bayar ya kai na mutun 844 da suka mutu. Sai dai kuma sun ce adadi zai iya karuwa da zaran masu ayyukan ceton sun kai ga sauran wuraran da basu samu kaiwa ba.

Wadanda suka tsira da rayukansu na fama da tarin matsaloli na rashin ruwa mai tsafta, da wutar lantarki da kuma abincin da zasu ci, sannan gidajen asibitoci sun cika sun batse da wadanda suka samu raukuna. Sai dai da yake jawabi ga manema labarai Sutopo Purwo Nugroho, mai magana da yawun ma'aikatar kula da iftila'i, ya ce kamfanin wutar lamntarki na kokarin dawo da wuta a yankunan:

"Jami'an ma'aikatar lantarki su kimanin 216 ne ke aiki tukuru, na ganin sun dawo da wuta cikin gaggawa, tuni an kawo manyan injimomin wuta guda takwas a yankunan Palu da kuma Dongara. Don haka ina ganin nan zuwa kwanaki biyu wuta za ta dawo."