1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Illar mayar da Jega shugaban INEC na jeka na yi ka

Zainab MohammedSeptember 4, 2012

Matakin da gwamnatin Najeriya ta dauka na karbe madafan ikon zartaswa daga hannun shugaban hukumar zabe mai zaman kanta farfesa Attahiru Jega ya haifar da martani da hasashen illar da hakan ka iya yi ga alkiblar INEC.

https://p.dw.com/p/163Ww
Attahiru Jega, Independent National Electoral Commission Chairman, declares Nigeria's incumbent President Goodluck Jonathan as the winner of last Saturday's presidential election, in Abuja, Nigeria, Monday, April 18, 2011. Jonathan clinched the oil-rich country's presidential election Monday, as rioting by opposition protesters in the Muslim north highlighted the religious and ethnic differences still dividing Africa's most populous nation. (Foto:Sunday Alamba/AP/dapd)
Hoto: AP

 Ministan shari'ar Najeriya ne ya  fito karara ya bayyana cewa daga yanzu shugaban hukumar zabe farfasa attahiru Jega ba shine ke da cikakken ikon tafiyar da harkokin hukumar zaben wadanda suka hada da harkokin kudi. Lamarin da ka iya mai da shi shugaba na jeka na yika. Amma sanin irin muhimmancin da hukumar zabe ke da shi a tsarin demokaradiyya irin ta Najeriya da saboda takadammar da ke tattare da gudanar da zabe, ya sanya Dr Kole Shatima masani a fanin kimiyyar siyasa bayyana yadda suke kalon wannan lamari.

‘'To wannan abin da ya taso  ya bamu mamaki  domin da mun yi tsammanin cewa shi shugaban hukumar zabe shine shugaba mai cikakken iko. To wannan ya zo ya daure mana kai domin kuwa yaya za'a ce mutum shine a wajen kuma shine shugaba amma bashi da cikakken iko? To wannan bambanci da shi ministan shari'a ya fitar da shi ya zo ya daurewa jama'a kai har suna ganin watakila dai akwai wani abu a kasa wanda bamu gane ba, wannan dai shine ke damun jama''.

Sai dai ga wasu 'yan siyasar Najeriya sun kasance masu ja da wannan ra'ayi bisa dalilan cewa a yanzu ne aka kama hanyar komawa kan bin ka'ida da zata iya taimaka a daidaita lamurra. Dr Yunusa  Tanko shine shugaban jamiyyar adawa ta NCP wanda ke  cikin masu marhabin da wannan sauyi da aka samu.

©Jonathan Rebboah/Wostok Press/Maxppp France, Paris 25/11/2011 Le president du Nigeria Goodluck Jonathan arrive au palais de l Elysee The President of Nigeria Goodluck Jonathan at the Elysee Palace
Hoto: picture alliance / dpa

‘'Tun da farko dama ai shi shugaban INEC bai da wannan karfin da aka bashi na farko, ai kwamishin ne kuma a tsarinta ko dai tana da darakta janar ko ,kuma sakatare ya kamata mutane su fahimci wannan. To laifin dama a kansu ne su shuwagabani da shugabanin inec. Wanna ba zai shafi zabe ba, rashin bin doka shi ya sa muka shiga kakanikayi. Dama can shi shugaban INEC ya karbi duk karfin gaba daya kan shine wuka shine nama, kuma ba haka ba ne.''

Illar karbe iko daga hannu farfesa Jega

Wannan sauyi dai ya faru ne a dai dai lokacin da Najeriya ke shirin gudanar da zaben shekara ta 2015 wanda tuni aka fara rige rigen neman iko a kansa: abinda ya sanya Dr Kole Shatimma bayyana tsoron illar da hakan ka iya yi.

‘'To illarsa dai da yawa: gashi muna ganin zaben shekara ta 2015 ana ta shirye shiryensa. To mutane da yawa suna ganin watakila ana yin wannan ne don a sa shi wannan shugaban ya bar aiki tun da ya zama shugaba na jeka na yikane, in yaso sai a sa wanda ita gwamnati take so. To wannan sai zai a yi zabe ne shugaba zai fito ya ce ga abubuwan da ya kamata a yi kuma sakataren ya ce ai ba shi ke da ikon wannan ba. To abubuwa da muke tsoro kenan.''

Attahiru Jega, Independent National Electoral Commission Chairman, reads the results sheet before he declared Nigeria's incumbent President Goodluck Jonathan as the winner of last Saturday's presidential election, in Abuja, Nigeria, Monday, April 18, 2011. Jonathan clinched the oil-rich country's presidential election Monday, as rioting by opposition protesters in the Muslim north highlighted the religious and ethnic differences still dividing Africa's most populous nation. (AP Photo/Sunday Alamba)
Hoto: AP

Sauyin da aka samu da ke zama koma baya ga yunkurin da farfesan Jega ya yi na kokarin ganin majalisar dokokin Najeriya ta yiwa dokar zabe ta 2010 gyaran fuska domin bashi Karin iko, ya sanya da kansa ya nemi minsitan shari'ar ya yi mashi filla filla abinda shari'a ta ce a kan wannan batu. Takadama da kokarin kame madafan iko a hukumomi da ma'aikatun gwamnati  gwamnati irin na hukumar zaben Najeriya lamari ne da ke tasiri sosai ga yadda ake tafiyar da harkokinsu. A yanzu wannan sauyi ya mikawa sakataren hukumar zama babban jami'in  kula da harkokin kudin a hukumar zaben Najeriya.

Mawallafi: Uwais Abubakar Idris
Edita: Mouhamadou Awal