1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Annobar corona ta janyo tashe-tashen hankula

Ramatu Garba Baba
June 17, 2021

Wani sabon rahoto na Global Peace Index ya nuna yadda aka samu karuwar tashe-tashen hankula a sassan duniya tun bayan bullar annobar corona.

https://p.dw.com/p/3v4fN
Bild des Jahres 2020 I England I Patrick Hutchinson I Waterloo station
Hoto: Dylan Martinez/REUTERS

Rahoton na Global Peace Index, ya nuna cewa annobar corona ta haifar da karuwar tashe-tashen hankula a sassan duniya. Nazarin da da masana suka yi, ya gano cewa, daga shekarar 2020, alkaluman tashe tashen hankulan sun kasance yadda suke a tsawon shekaru goma sha biyu da suka gabata. 

Duk da cewa an sami raguwar aiyukan ta'addanci a bara inji rahoton, amma an gudanar da munanan zanga-zangar da aka zubar da jini da tafka asarar rayuka, rahoton ya daura nauyin aukuwar hakan kan annobar ta corona.

Kasashen da aka gudanar da zanga-zangar da suka janyo asarar rayuka da dukiya sun hada da Belarus da Myanmar da Rasha inda jami'an tsaro suka yi amfani da karfi a murkushe masu boren, sai kuma zangar zangar Black Lives Matters a Amirka da samamen da magoya bayan tsohon shugaban Amirka Donald Trump suka kai kan majalisar kasar.